page 27.indd

27
AMINIYA
Juma’a, 2 ga Janairu, 2015
SIYASA
Yanzu ba a sayen mutane a siyasa
– Mace ’yar takarar Gwamna
Sanata A’isha Jummai Alhassan
Sanata ce daga Jihar Taraba,
kuma a halin yanzu ita ce mace
’yar takarar Gwamna a Jihar
Taraba a qarqashin Jam’iyyar
APC. A wannan tattaunawa da
ta yi da Aminiya ta yi bayanin
dangantakarta da xan takarar
Shugaban Qasa a Jam’iyyar
APC Janar Buhari da kuma
dambarwar siyasar da ke gudana
a Jihar Taraba. Ga yadda hirar ta
kasance:
Daga Magaji Isa, Jalingo
Aminiya: Ana raxe-raxin cewa akwai
rashin jituwa tsakaninki da xan takarar
Shugaban Qasa na Jam’iyyar APC Janar
Muhammadu Buhari, mene ne gaskiyar
wannan lamari?
A’isha Alhassan: Wannan ba gaskiya ba
ne, akwai kyakkyawar fahimta tsakanina
da Janar Muhammadu Buhari, domin duk
lokacin da na haxu shi nakan durqusa in
gaishe shi. Bari in faxa maka, duk lokacin
da shi Janar ya gan ni abin da yake fara
kirana da shi shi ne “Gwamnata,” kafin ma
mu soma gaisuwa. Ni kuma sai in ce lafiya
lau Sa, saboda haka akwai kyakkyawar
fahimta tsakanina da Janar Buhari.
Kuma siyasa ba yaqi ba ne ko kuma
abin gaba, duk da kasancewar ban yi
shi ba a lokacin zaven fidda xan takarar
Shugaban Qasa na jam’iyyarmu ta APC
da aka gudanar a garin Legas, amma Janar
Buhari bayan mun dawo daga Legas ya tafi
gidan xan takarana Alhaji Atiku Abubakar
a Abuja ya gode masa ya kuma nemi haxin
kansa. Ni ba ni da wani abu a zuciyata, wato
ba ni da wata qullaliiya ko gaba da Janar
Muhammadu Buhari. A zaven shekarar
2011 ina cikin Jam’iyyar PDP, amma Janar
Buhari na zava, saboda wani dalili na
qashin kaina.
Aminiya: To me ya kawo wannan
zargin?
A’isha Alhassan: Wannan aikin jahilan
’yan siyana ne waxanda ke yin gaba da
waxanda ba su zavi wani xan takara ba. In
ban da jahilci, ya kamata a ce daga ranar
da aka zavi Janar Buhari a matsayin xan
takarar Shugaban Qasa, to a ce babu sauran
maganar ofishin kamfen na Janar Buhari.
Abin da ya kamata shi ne, a maida
hankali wajen gudanar da kamfen don
ganin Janar Muhammadu Buhari ya samu
nasara, ba wai ka-ce-na-ce ba, kamar abun
da ke faruwa a Jihar Taraba. Saboda haka
idan su jahilan ’yan siyasa ne shi Janar
n Sanata A’isha Jummai Alhassan
Buhari ba jahilin xan siyasa ba ne.Kuma ya
kamata jama’a su san matsayina a kan Janar
Muhammadu Buhari, shi uba ne a gare ni,
kuma shi ne xan takarar Shugaban Qasa na
jamiyyarmu. Zan bayar da gudunmawata
ga kamfen xinsa domin ganin Janar Buhari
ya lashe zave saboda in qara jaddada cewa
ba ni da wata matsala da Janar Buhari, yana
goyon bayana, ni kuma ina goyon bayansa.
Aminiya: Wasu mutanen ofishin
kamfen na Janar Buhari a Jihar Taraba
sun ce ba a yi zaven gaskiya ba a lokacin
da aka zave ki a matsayin ’yar takarar
Gwamna na Jam’iyyar APC a jihar. Me
za ki ce?
A’isha Alhassa: Idan za a yi zaven fidda
da xan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC
a Jihar Taraba sau xari zan lashe zaven.
Duk wanda ya kasance a inda aka gudanar
da zaven fidda xan takarar Gwamna na
jam’iyyarmu ta APC a Jalingo ya san cewa
zave ne na gaskiya aka yi, ba wai xauki xora
ba, babu wani maguxi, ko faifan bidiyo na
zaven yana nan, saboda haka ba a voye aka
yi wannan zave ba.
Kamar yadda kowa ya sani, kowane
wakili ya kaxa quri’arsa a lokacin zaven
, waxanda suka faxi zave ne suke irin
waxannan maganganu marasa tushe
domin su kawo ruxani a tafiyar da muke
yi. Ya kamata irin waxannan mutane su
sani cewa yanzu an daina siyasar kuxi.
Waxannan ’yan takara da ba su yi nasara
ba, ba sa tare da jama’a. Sun daxe ba su zo
Jihar Taraba ba, sai kawai da zave ya qarato
suka shigo Taraba, akwai wani xan takara
ma kwana huxu kacal ya rage a yi zave ya
shigo garin Jalingo.
Yanzu ba a sayen mutane a siyasa,
mutane suna tare da wanda yake tare
da su ne, ba wai kawai sai lokacin zave
mutum ya xauko kuxi ya ce yana neman
ya sayi jama’a ba. Abin da ya kamata
waxannan ’yan siyasa su yi shi ne su natsu
su gano inda suka yi kuskure su gyara
don gaba. Amma sun kasa yin haka sai
surutan banza. Ina qara nanata cewa idan
za a yi zaven fidda ’yan takara sau xari
zan yi nasara, domin ina tare da mutane,
mutane suna tare da ni.
Waxansu daga cikin waxanda suka
faxi zave sun raba kuxi, amma an qi
zavensu, daga cikinsu akwai waxanda
suka bayar da Naira dubu talatin da biyar,
waxansu kuma sun bayar da Naira dubu
ashirin da biyar, amma an qi zaven su
domin ba sa tare da jama’a.
Aminiya: Ana zargin cewa qafarki
xaya na cikin Jam’iyyar APC ne xaya
kuma na cikin Jam’iyyar PDP, haka ne?
A’isha Alhassan: Ana yin wannan
zargin ne don na je taryar Alhaji Sani
Abubakar Xanladi a lokacin da ya
iso Jalingo bayan Kotun Qoli ta bayar
da umurnin cewa a maida shi kan
muqaminsa. Tun kafin a tuve shi akwai
kyakkyawar dangantaka tsakanina
da shi, kuma a da can a Jam’iyyar PDP
muke, sannan a lokacin da na tsaya
takarar Sanata na mazavar Taraba ta
Tsakiya ya taimaka mini na ci zave.
Abu na biyu shi ne, xaya daga cikin
dalilan da Xanbaba Suntai ya kawo don
a tsige Alhaji Sani Xanladi shi ne, wai ni
da shi da Sanata Tutare Abubakar mun
haxu mun kitsa yadda za mu kashe shi
Xanbaba Suntai a lokacin da muka tafi
aiki Umara a qasar Saudiyya. A zahirin
gaskiya ba mu haxu da Sani Xanladi a
qasar Saudiyya ba, domin a ranar da na
bar qasar Saudiyya a ranar ce shi kuma
Sani Xanladi ya isa qasar.
To, ganin dukkan dalilan da aka
bayar a matsayin hujjar cire Alhaji Sani
Xanladi duk qarya ne, sai na kira ’yan
majalisar Jihar Taraba xaya da xaya na
ba su shawarar cewa wannan abin da
suke so su yi, ba gaskiya ba ne, kuma
zai iya kawo rigima a jihar, amma suka
qi jin shawarata. Kowa ya san cewa ba
a bi gaskiya ba wajan tsige Alhaji Sani
Abubakar Xanladi.
Bayan wannan kuma lokacin da ya
yi gudun hijira ya zo Abuja, yakan zo
ya gaida da ni, ni ban kashe ko kwabo
a wajen shari’arsa ba, amma na taya shi
addu’a wajen ganin Allah Ya taimake shi
ya samu haqqinsa da aka tauye ta hanyar
tsige shi da aka yi ba a kan qa’ida ba.
Sannan kuma ya kamata ka fahimce
cewa an yi haka ne don wanda aka tsige a
kan muqaminsa a shafa masa kashin kaji
a hana shi ya tsaya takara har sai bayan
shekara goma.
Kamar yadda na faxi tun farko cewa
akwai fahimta kyakkyawa a tsakanina
da shi, saboda haka ashe bai zama laifi
ba, idan na taya wannan mutum murna
bayan ya samu nasara a kotu.
Ya kamata kowa ya san cewa, in don
na je taryar Alhaji Sani Xanladi shi ne
laifi, to na yi laifin kuma Alhaji Sani
Xanladi ya dawo Jihar Taraba a matsayin
Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba,
kuma ni Sanata ce wadda ke wakiltar
mahaifarsa, saboda haka ban ga wani
laifin yin haka ba.