page 23.indd

Zinariya 23
AMINIYA
Juma’a,2 ga Janairu, 2015
Sanyin idon kowace mace
IYAYEN GIJI
Mata da cututtukan zamani
Abubakar Haruna, Daga Legas
A
ci gaba da nazari da muke
yi a kan mata da cututtukan
zamani a wanannn mako
za mu dubu yadda jahilci
da kunya ke sanyawa mafi yawan mata
suke faxawa cikin tarkon kamuwa da
cututtuka masu yawa a wannan zamanin
da muke ciki.
Da dama daga matanmu sun jahilci
yadda ake kamuwa da irin waxannan
cututtuka, kamar cutar sanyi irin su
gonoriya da tsargiya da yankan gashi
da sauransu, waxanda suke haddasa
qaiqayin gaba da quraje da fitar ruwa
daga gaban mace ko namiji da wari farjin
mace da savar azzakari da qanqacewar
azzakari da kumburin farji da azzakari
da sauran su.
Babu shakka mafi yawan mata sun
kamu da irin waxannan cututtuka, amma
sai kunya ta hana su bayyanawa don a
nema musu magani. Idan matar aure ce
sai ka ga ta voye wa mjinta don jin tsoron
kada ya zarge ta da fasiqanci, idan kuwa
budurwa ce sai ita ma ta voye wa saurayin
da zai aure ta saboda tsoron sakamakon
abin da zai haifar.
Ba komai ke janyo wa mata suke voye
kamuwa da cututtukan ba sai tsabar
jahilci, domin idan da sun san haxarin
barin cutar a jikin xan Adam da sun yi
gaggawar bayyanawa domin a gaggauta
nema musu magani. Wani abin mamaki
shi ne za ka ga yarinya budurwa tana
fama da irin waxannan cututtuka, amma
sai ka ga ta voye wa mahaifiyarta duk da
irin shaquwar da suka yi. Haka za a yi
mata aure ba tare da sanin iyayenta ba
ko saurayin da ya aure ta, sai daga bisani
idan mijin ya kamu a riqa kame-kamen
yadda za a yi maganin abin.
Wata kuwa saboda tsabar jahilci sai ta
riqa bin qawayenta tana gaya musu tana
tsammanin za su taimaka mata, amma
daga bisani sai su ci amanarta su riqa yaxa
ta a duniya har ya kai idan wani saurayi ya
fito zai aure ta su gaya masa cewa tana da
ciwon sanyi. Shi ya sa shawarar da nake
bai wa mata ita ce duk lokacin da suka
DUNIYAR MA’AURATA
fahimci sun kamu da xaya daga cikin
waxannan cututtuka, to su natsu, kada
su tayar da hankalinsu, su tafi asibiti kai
tsaye a auna su a tabbatar da irin dangin
ciwon sanyin da yake damun su, ta yadda
za a san maganin da za a ba su. Wannan
shi zai sanya su ma su san irin nau’in
cutar sanyin da take damun su.
Wani abin lura shi ne babban dalilin
da ya sa wasu matan suke voye cutar shi
ne gudun tsangwama daga waxanda ke
tare da su, kamar iyaye da ’yan’uwa. Don
mafi yawan jama’armu idan aka yi zancen
ciwon sanyi abin da suke fara tunani shi
ne, mutum ya xauka ne ta hanyar banza
kamar jima’i.
Tare da Nabeela Ibrahim Khaleel
Tambayoyin Duniyar Ma’aurata 7
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haxuwa
cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo
cikinsa, amin. Ga ci gaba akan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko,
da fatan Allah yasa wannan bayani ya isa ga duk masu buqatarsa, musamman
waxanda suka aiko da tambayoyin, amin.
T
ambaya Ta 17: Na ji kun ce Mala’i’ku ba su
shiga gidan da yake da hoto, wane irin hoto
ke nan, hoton Maigida da Iyalansa? Ina
neman qarin bayani.
Amsa: Annabi SAW ne ya faxi haka; cewar Mala’iku
ba su shiga gidan da cikinsa akwai hoto, zane ko
taswirar dukkan wani abu mai rai. Wannan ya zo a
cikin ingantaccen Hadisin da aka ruwaito daga Uwar
Muminai Aishah RA. Amma ba laifi akan hotunan
furanni da shuke-shuke.
Tambaya Ta 18: Ina tambaya ne game da amfani da
baki wajen ibadar aure: Kun ce waxansu Malamai sun
ce ba haramun ba ne, sai dai in maniyyi ko maziyyi ya
shiga baki sannan ya zama haram. Shin sai an haxiye
ne ko kuma a baki kawai? Domin waxansu sun ce sai
an hadiye ne zai zama haram; don Allah ina son qarin
bayani.
---Dahiru Umaru.
Amsa: Kamar yadda bayani ya gabata cewa,
wani vangaren na Malamai na xaukar maniyyi
da dangoginshi a matsayin qazanta kawai (watau
khaba’ith). Shigar maniyyi da dangoginsa cikin baki
haramun ne, domin su xin abubuwan qazanta ne,
bakin xan Adam kuwa ba wurin sanya abubuwan
qazanta ba ne, don haka ba inda shari’a ta amince da
shigar abin qazanta cikin baki. Allah SWT ya haramta
mana ci ko shan abubuwan qazanta a cikin Al’qur’ani
Mai girma; misali, a cikin Aya ta 157 cikin Suratul
A’araf:
“Kuma Shi (Allah Maxaukaki) Ya haramta musu
abubuwan qazanta…”
Don haka dole ma’aurata su kiyaye kar waxannan
abubuwa suna shiga cikin bakunansu, har in ya zamar
musu dole sai sunyi haka xin; da fatan Allah Ya bada
ikon kiyayewa, amin.
Tambaya Ta 19: Ina so ku gaya min yadda zan shawo
kan Maigidana don ya rinqa dawowa gida da wuri.
Amsa: Ga shawarwarwarin duniyar ma’aura gareki:
1. Abu farko shi ne ki yi haquri, kuma ki qara ba
kanki haquri; ki sani kowane xan Adam yana da wasu
buqatu da uzurorin da suka sha bamban da na wani
xan Adam xin; kuma waxanda sun riga sun rikixe da
xabi’unsa, ta yadda zai yi wuya ya iya rabuwa ko daina
aikata su farat xaya komin yadda aka so haka xin. Don
haka kyakykyawan haquri, shi ne magani na farko.
2. Addu’a tana maganin dukkan matsalolin rayuwa;
don haka sai ki dage da yi masa addu’a a kowane lokaci,
kum musamman a lokuttan amsar addu’a: kamar cikin
sujjudar Salloli da lokacin zaman tahiya kafin sallama
da ranar Juma’a bayan Sallar La’asar da sauransu.
Sannan ki dage wajen tsaidawa da kyautata ibadarki da
yawan yin nafiloli, musamman na azumi da tsayuwar
Saboda haka ya kamata jama’a su
daina ruxewa don sun kamu da wata
cuta, abin da ya kamata mutum ya yi shi
ne, ya tafi asibiti a auna shi, a tattabar
da nau’in cutar, kuma ya nemi maganin
bature, idan na bature bai karve shi ba, to
ya gwada na musulunci ko na gargajiya.
Da yardar Allah zai samu lafiya.
Amma kuma ya kamata mutane su
riqa kiyaye hanyoyin da ake xaukar
waxannan cututtuka kuma su tsare kansu
da iyalensu sannan kuma a guji jita-jita.
Abubakar Haruna ya rubuto daga Legas
08027406827 abubakarharuna2003@
gmail.com.
[email protected] 08063675635
(TES KAWAI): Facebook/Duniyar Ma’aurata
dare, in sha Allahu za ki samu biyan buqatarki.
3. Ki sani, mafi yawa daga mazaje sun fi son zaman
waje akan zaman cikin gida, wannan wani abu ne da ya
samo asali daga ainihin gundarin halayyar xa namiji.
Don haka in dai ba wani aikin ashsha ne yake sa shi
daxewa a waje ba, to ki yi haquri, ki bi shi a hankali har
Allah Yasa ya rage daxewa a waje sosai.
4. Ki daina jin haushin mijinki saboda wannan
xabi’a akan wannan xabi’a da yake yi da baki so,
matuqar kina jin haushin abin, kuma kina bayyanar
masa da jin haushin, to wannan ba zai sa ya daina ba,
sai dai ya qara ingiza shi ma ga aikatawa.
5. Kar ki rinqa yawan damunsa da mita da qorafin
bai dawowa da wuri, in zai tafi ki yi masa rakiya, kina
mai masa addu’ar Allah Yasa a dawo lafiya cikin sakin
fuska da annashuwa. In ya dawo kuma ki tarbe shi cikin
sakin fuska da annaashuwa, tare da gabatar masa da
dukkan abin da kika san yana buqata a wannan lokaci.
6. Ki binciki kanki da yanayin zaman ku da shi
bincike mai zurfi, wataqila akwai wani abu da kike yi
masa wanda yasa bai son zaman gida, kamar in kina
damunsa da yawan mita da qorafi, ko ba ki gyara gidan
ki ko yanayin yadda gidan yake ne yasa bai son zama,
duk abin da kika lura yana da nasaba da matsalar sai
ki yi dukkan qoqarin da ya kamata ki ga cewa wannan
abin ya daina faruwa.
7. Ki duba cikin ma’ajiyarki ‘yammatacinki, ki
binciko hanyoyin qayatarwa da nishaxanwar da za ki
rinqa gabatar masa, ta yadda zai ji bai ma son fita wajen
ya fi son kasancewa tare da ke.
Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Yasa
mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.